FREE ONLINE EARNINGS 🪙💰🪙

Tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka a rubu'i na biyu na 2025 - NBS 💰


Tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka a rubu'i na biyu na 2025 


Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙara da kashi 4.23 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki.

Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48 idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na ingantuwar tattalin arzikin ƙasar.

Hukumar ta NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wana ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024.

Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana'antu da, da fan fetur da kuma fannin ma'adinai.


NBS ta ce a rubu'i na biyu na shekarar 2025, arzikin cikin gida da Najeriya ta samu ya kai naira tiriliyan 100.73, ƙari kan naira tiriliyan 84.48 da aka samu a 2024 daidai wannan lokacin, abin da ke nuna ƙarin kashi 19.23 cikin 100.



Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form