NAZARIN GOOGLE DA CHATGPT AI KENAN

 

Ana Wata, Ga Wata..!

Yakin neman iko a duniyar Artificial Intelligence ya zanza salo, bayan kamfanin Google sun saki sabon AI din su mai suna Google BARD, wanda masana ilimin prompt sun tabbatar ya dame ya kuma shanye AI din kamfanin OpenAI da Microsoft, wato ChatGPT4.


Sai dai kuma wasu masu nazari a duniyar AI din sun ce: Har yanzu fa ba'a saki kaso 10% cikin darin abinda ChatGPT zai iya ba, kamfanin OpenAi da Microsoft suna sane da cewa dama kamfanin Google zasu musu wannan tsiyar, shiyasa suka saki kadan cikin abinda AI din nasu zai iya.


Sai dai kuma daga bangare guda wasu masu nazarin na ganin cewa: Maganar fa ace dama kamfanin OpenAI da Microsoft zasu danne Google a fannin AI abu ne da kwata-kwata bai taso ba, saboda shirin kirkirar AI Google sun yisa tun shekarar 2016 suka fara yi.

Sun rufe binkicen ne da kimiyyar bayan Robot din da suka kirkira na AI ya fara training ma kansa wani sabon yare, wanda su kansu masu kirkirar basu fahimci yaren ba. Wannan ne dalilin da yasa aka rufe wannan shirin, saboda ana tsoron me zai iya zuwa ya dawo.


Bugu da kari babban abinda ake buqata wajen kirkirar AI shine information, kuma google yana da iya information na mutane wanda yakai Gigabyte Biliyan 27, wannan information din sun hada da rubutu, hotuna, videos, location, password, human activities, email, notification, voice recording duk abinda ka fada wayarka tana sauraronka dss.


Abinda baka sani ba har wannan rubutun da nayi google ya dauka ya sani, kai har comment din da zaka mini. Matuqar da wayar Andriod kayi, toh sai shehi Google yayi saving. Duk wani motsin rayuwarka google ya sani, har abinda ka labe kayi kai kadai. Shiyasa masana ke cewa yadda google ya san mu, Allah ne kadai ya san mu fiye da haka.


Da wannan dalilin ne wasu masu nazarin ke ganin zai wuya a danne Google a wannan tseren. Sai dai maybe bamu san abinda OpenAI da Microsoft suka taka ba. Kai Google Bard ya ninka kwakwalwar dan Adam sauri sau dubu dari,


Kai tsaye zaka iya zuwa kayi register ka fara amfani da Google Bard yanzu, kawai kaje Chrome ka rubuta Google Bard zai baka link din farko sai ka shiga kayi register. 


ABBALO MBC SEO MANAGER 
HAUSA HACKME 

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form